– Fadar shugaban kasa ta yi watsi da da’awar cewa Buhari na da wani manufa a kan alkalan da aka kama kwanan nan
– Mai Magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu yace shugaban kasa bai taba neman alfarma a gurin alkalai ba
– Shehu ya bayyana cewa Buhari zai zama mutum na karshe da zai umarci wani ya tozarta mai hukunci don kawai ya karkatar da gaskiya
Fadar shugaban kasa ya gargadi yan jarida da sauran yan Najeriya da su daina danganta shugaban kasa Muhamamdu Buhari da take hakkin wasu alkalai da hukumar yan sandan farar hula (DSS), suka kama kwanan nan, jaridar Vanguard ta ruwaito.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da akayi a jiya, Litinin, 31 ga watan Oktoba a Abuja, daga Mallam Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin labarai da zumunta.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Kebbi da tawagarsa sun ziyarci gonan shinkafa
Shehu yace: “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai kasance mutun na karshe da zaiyi umaurnin wani ya take hakkin alkalai don kawai ya karkatar da gaskiya.
“Duk da cewan ya san wasu alkalai, shugaban kasa bait aba neman alfarma daga hannunsu ba; tun shekara ta 2003, 2007 da kuma 2011, lokacin da ya fuskanci kalubalan zanba na sakamakon zaben shugabancin kasa, daga kanana zuwa manyan kotuna a kasar.
KU KARANTA KUMA: Talauci ke haddasa sace-sacen mutane, ta’addanci- Dangote
“A matsayinsa na dan siyasa, Buhari bait aba shawartan Lauyansa da ya tunkari ko wani alkali don neman taimako don cin nasara a kan shari’ar sa ba. Shugaban kasa na bin tsarin wannan ka’ida kuma bai taba sabawa ga hakan ba.
Kan maganan alkalai dake fuskantar tuhuma kan aikata rashawa, Shehu yace: “shugaban kasa bai fada ma kotu yadda zasuyi aikinsu ba kuma cewa duk wanda aka zarga da sikata rashawa kotu bat aba mai shi kariya ba kuma shine zai tabbatar da gaskiyan sa.”
Daya daga cikin wadanda aka kama alkalin babban kotu, Justis Sylvester Ngwuta, a cikin wata wasika da aka rubuta a ranar 18 ga watan Oktoba, wanda ya mika ga alkalin alkalai na Najeriya, Justis Mahmus Mohammed da kungiyar alkalai na kasa, ya zargi Rotimi Ameachi, ministan sufuri da kuma Dr. Ogbonnaya Onu, ministan kimiya a matsayin wadanda suka tunkare sa a madadin jam’iyyar APC, da ya taimaka ya juyar da gaskiyan zaben gwamna a jihohin Ekiti, Rivers da kuma Ebonyi.
The post Fadar shugaban kasa ta maida martani kan zargin Buhari da bada umarnin kama alkalai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Comments
Post a Comment
We love to hear from you!
Sign in to comment "anonymously" without entering verification text.