– Sojojin Najeriya sunce kimanin ‘yan kungiyar Boko Haram guda 240 ne suka mika wuya a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba
– Sojojin suce yan ta’addan sun mika wuya ne ga wani rundunar hadin gwiwa wato Multi National Joint Task Force (MNJTF)
– Yan ta’addan sun mika wuya ne tare da iyalansu
Hoton wasu yan Boko Haram da sojojin Najeriya
Kimanin ‘Yan Boko Haram 240 suka mika wuya ga sojojin Najeriya bayan sun sha luguden wuta ta kasa da sama daga rundunar hadin guiwa ta MNJTF a wani farmakin da ta kaddamar mai taken Gama Aiki.
KU KARANTA KUMA: Buhari baida nasaba ga kamun alkalai- Fadar shugaban kasa
Jami’in hulda da jama’a na rundunar hadin guiwar Muhammad Dole ya fadi a cikin wata sanarwa cewa ‘Yan ta’addar na Boko Haram da iyalansu sun mika wuya tare da makamansu bayan sun sha wahala a farmakin da aka kaddamar akansu.
Kanal Dole ya ce mayakan sun mika wuya ne a garin Bagasola a cikin Chadi.
Babban kwamandan rundunar hadin guiwar ta MNJTF Janar Lamidi Adeoson da ya ziyarci sansanin da aka ajiye ‘Yan Boko Haram da suka mika wuya a Bagasole, ya yaba akan karfin halin da suka yi na yanke shawarar yin watsi da ta’addanci.
Janar Adeosun ya kuma bukaci su ja hankalin sauran ‘Yan uwansu da ke daji su daina fada domin kofa a bude take su mika wuya.
The post Labari da dumi-dumi! ‘Yan Boko Haram 240 sun mika wuya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Comments
Post a Comment
We love to hear from you!
Sign in to comment "anonymously" without entering verification text.