– Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawari amma kuma ya saba
– Shugaban Kasa yayi alkawarin daukar matasa 200,000 aiki kafin karshen watan Jiya, amma har yau ba labari
– Wani Farfesa a Amurka, Farouk Kperogi ya koka da wannan abu
Farooq Kperogi
Farfesa Farouk Kperogi da ke Jami’ar Jihar Kennesaw ta Kasar Amurka ya bayyana ta shafin san a Facebook cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karya alkawarin da yayi. Shugaban Kasa Buhari yayi alkawarin daukar matasa aiki kafin karshen watan Jiya, amma har an shiga sabon wata, shiru kake ji.
Farfesa Kperogi ya nuna damuwar sa da halin da ake ciki a mulkin Shugaba Buhari, ya kuma nuna takaicin ga yadda matasa da dama suke zaune ba aikin yi a Kasar nan. Kwanakin baya Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa Gwmanatin Tarayya ta fara tantance matasa 200,000 da za ta samarwa aiki a Kasar.
KU KARANTA: Abin da ya hana mu kama Jonathan-Shugaban Kasa
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce zuwa karshen watan Oktoba za a samarwa matasa 200,000 aiki a Najeriya, Farfesa Kperogi yace shin ina matasan da aka samawa aikin, ganin watan Oktoba ta kare?
Farfesa Kperogi ya bada labarin yadda wasu dubunnai suka rasa ayyukan su a Kasar. Yace ya samu sako daga wani cewa yana cikin mutane fiye da 1300 da aka kora daga aiki, Farfesa Kperogi yace wannan abu akwai takaici. Farfesa Kperogi yace dole Gwamnatin Tarayya ta zage dantse, a fara gani a kasa.
The post Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saba alkawari, inji shahararren Farfesa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Comments
Post a Comment
We love to hear from you!
Sign in to comment "anonymously" without entering verification text.