Za a iya samun cikas wajen tattaunawar sulhu da Neja-Delta

– Wani ja-gaba wajen harkar gwagwarmayar Neja-Delta, P Bebenimibo yace akwai yiwuwar a samu matsala a tattaunawar Gwamnati da Neja-Delta

– Yace babu wani zama da za ayi, yayi aiki ba tare da Tompolo ba

– Bebenimibo yace yayi farin cikin ganin Gwamnatin ta zauna da manyan Yankin na Neja-Delta

Tsagerun Neja-Delta

Kwamared Paul Bebenimibo, wanda fitacce ne a yankin Neja-Delta yace duk wata tattaunawa da za ayi tsakanin Gwamnatin Shugaba Buhari da Mutanen Yankin Neja-Delta ba zai kai ga ci ba idan har ba a zauna da Government Ekpemupolo ba, wanda aka fi sani da Tompolo.

Paul Bebenimibo ya bayyanawa manema labarai na jaridar The Nations cewa mafi yawan mutanen da Gwamnati ta ke tattaunawa da su, ba su san ainihin lamarin ba. Bebenimibo ya bayyana cewa Tompolo ne ya san ciki da ban Yankin na Neja-Delta, ya dai yi wannan  bayani ne a jiya Litinin.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe dan Boko Haram

Kwamared Bebenimibo ya kuma bayyana cewa yayi farin cikin ganin an zauna domin tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya ta Shugaba Buhari da mutanen Yankin na Neja-Delta mai arzikin man Kasar. Bebenimibo yace amma fa Gwamnati ta san cewa sai ta hada da mutane irin su Tompolo, domin su suka san Neja-Delta, kuma su za su iya maganin duk wata matsala.

A Yau Talata, Shugaba Buhari zai kara tattaunawa da wasu Manyan Yankin na Neja-Delta. Gwamnatin Kasar dai tana neman shi wannan mutumi Tompolo, ruwa a jallo da laifi.

The post Za a iya samun cikas wajen tattaunawar sulhu da Neja-Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Comments